Home Labarai Ma’aikatan NIMC sun shiga yajin aiki

Ma’aikatan NIMC sun shiga yajin aiki

171
0

A yayin da ƴan Nijeriya ke rige-rigen yin rajistar katin shaidar zama dan kasa, ma’aikatan hukumar NIMC mai kula da yin rajistar sun tsunduma yajin aiki.

Ma’aikatan sun fara yajin aikin ne a safiyar ranar Alhamis, yayin da wa’adin da gwamnatin tarayya ta bayar na rufe layukan wayan da ba a yi wa rajista da lambar NIN ba ke kara matsowa.

Kungiyar ma’aikatan ta ce, “Kwamitin Zartarwa Reshen NIMCI na umartar ma’aikata daga mataki na 12 zuwa kasa a Shelkwata da rasssan jihohi da su yi zamansu a gida daga yau 7 ga Janairu 2021.

“Muna kuma shawartar mutane da su kaurace wa ofisoshin NIMC na kananan hukumomi da sauran cibiyoyi domin jami’an kwamitin aiki da cikawa za su zaga domin tabbatar da wannan umarni,” inji sanarwar da Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati Reshen NIMC, Asekokhai Lucky Michael da Sakatarensa, Odia Victor suka fitar.

Ma’aikatan sun dauki matakin ne domin tabbatar biyan bukatunsu da suka hada da kariyarsu daga cutar COVID-19 da kuma biyan su sabon albashi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply