An rantsar da sabuwar shugabar jami’ar Calabar, wato (UniCal), Farfesa Florence Banku-Obi.
Farfesa Banku-Obi ita ce mace ta farko kuma ta goma sha daya a jerin masu rike da mukamin shugabancin jami’ar bayan shekaru 45 da kafa ta.
A Talatar nan ne dai Farfesa Zana Akpagu, wanda wa’adin mulkinsa ya kare a ranar 30 ga Nuwamba ya mika ragamar shugabancin jami’ar ga Farfesa Obi.
