Home Coronavirus Madagascar 🇲🇬 ta yiwa Nijeriya 🇳🇬 ta yin maganin Covid-19

Madagascar 🇲🇬 ta yiwa Nijeriya 🇳🇬 ta yin maganin Covid-19

221
0

Jamhuriyar Madagascar, ta yi tayin maganin gargajiyar ta kan coronavirus ga Nijeriya da sauran kasashen Afirika.

An dai aike da kason Nijeriya na maganin ne a Equatorial Guinea, kuma daga nan ne, za a yi jigilar sa zuwa Abuja.

Gwamnatin tarayyar Nijeriya dai na fuskantar matsin lamba, kan ta bar cibiyar binciken hada magunguna ta kasar da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta yi binciken kimiyya kan maganin.

Wasu kuma na kokarin ganin an gudanar da gwaji kafin yin amfani da maganin a kasar.

Idan dai za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa har yanzu bata tabbatar da sahihancin maganin ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply