Home Coronavirus Madagascar na son Nijeriya ta biya ta €170,000 na maganin Covid-19

Madagascar na son Nijeriya ta biya ta €170,000 na maganin Covid-19

175
0

Jamhuriyar Madagascar ta bukaci Nijeriya ta biya Euro 170,000 na kudin maganin Covid-19 da ta aikewa gwamnatin tarayya.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai, ba a iya tantance adadin yawan maganin da kasar ta aikewa Nijeriya ba, wanda ya biyo ta Guinea Bissau.

Shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo, wanda ya ziyarci shugaba Buhar a fadar sa, a karshen mako ne, ya kawo maganin da Madagascar ta aikewa Nijeriya.

Shugaba Buhari, tun da farko dai, ya ce Nijeriya za ta gudanar da binciken kwakwaf kan maganin don tabbatar da ingancin sa.

Wata majiya ta ce a ranar Lahadi ne Nijeriya ta samu bayanan biyan kudin, wanda ke nuna kasa na tabbatar masu ba kyauta ta basu maganin ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply