Home Labarai Mafi ƙarancin Albashi: hukumomi 428 ba za su iya biyan albashi ba

Mafi ƙarancin Albashi: hukumomi 428 ba za su iya biyan albashi ba

171
0

Gwamnatin tarayya ta ce kimanin hukumomin gwamnati 428 ne ba za su iya biyan albashi ba, daga nan zuwa ƙarshen watan Nuwamba.

Babban Daraktan Ofishin kasafi Ben Akabueze ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin kula da asusun gwamnati na majalisar Dattawa a ranar Talata.

Ya ce wannan ya faru ne sakamakon gwamnatin tarayya ta shirya kasafin kuɗin shekarar 2019 kafin a sanar da sabon tsarin albashi mafi ƙaranci.

Saidai ya ce gwamnatin na shirin sakin wasu kuɗi da za su taimaka wajen toshe wannan matsala ta albashi, a watan na Nuwamba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply