Home Labarai Mafi yawan yaran Nijeriya ba su da takardar haihuwa – Rahoto

Mafi yawan yaran Nijeriya ba su da takardar haihuwa – Rahoto

136
0

Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya yi la’akarin cewa kusan kaso 57% na yaran Nijeriya ‘yan kasa da shekaru 5 ba su da takardar haihuwa.

Da ya ke magana a wajen taron bita na ma’aikatan lafiya a birnin Awka na jihar Anambra, mai kula da ofishin UNICEF shiyya ta 1, Victor Atuchukwu ya ce kowane yaro nada damar mallakar takardar haihuwa, sai dai abin takaici mafi yawan iyaye, na yin biris da hakan.

Ya bukaci ma’aikatan lafiya da su rika tabbatar da cewa an yi wa kowane jinjiri takardar haihuwa ta yadda za a iya amfani da bayanan wajen tsara tattalin arzikin kasa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply