Wani bincike da jaridar “Daily Trust” ta gudanar, ya nuna cewa akwai ‘yan Nijeriya da dama da ba su da masaniya a kan wuraren da ake gudanar da gwajin cutar corona, bare ma har su je a auna su.
Har a ranar Talatar nan, sama da mutane 80,000 ne aka gwada a kan cutar a ya yin da 1,236 suka mutu da kuma 67,000 suka warke.
Rahotanni dai sun nuna cewa Nijeriya nada yawan mutane sama da milyan 200, kuma bai fi kaso 1% da aka gwada ba, a cibiyoyin gwajin cutar 69 da ake da su.
Kamar dai sauran kasashe, Nijeriya ma ta harbu da zagaye na biyu na cutar corona.
