Home Lafiya Maganin Jabu: Hukumar NAFDAC ta ce maganin jabu na kisa a boye

Maganin Jabu: Hukumar NAFDAC ta ce maganin jabu na kisa a boye

121
0

Daga Hannatu Mani Abu

Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna a Nijeriya, NAFDAC ta ce ‘yan Nijeriya na ci gaba da mu’amulla da magungunan jabu, galibi ba tare da saninsu ba. Farfesa Mojisola Adeyeye shugabar hukumar ce ta yi wannan karin hasken ga ‘yan jaridu masu bayar da rahotannin kiwon lafiya.

Farfesa Mojisola ta ce a sakamakon wannan mummunar dabi’a da wasu batagari ke dabbakawa, magungunan jabu sun yi sanadiyyar mutuwar ‘yan Nijeriya da dama.

 

Ta ce abin takaici duk da irin kokarin da suke yi na magance matsalar amma wasu sai su bi ta bayan fage su aikata laifin baza magunguna na jabu. Shugabar NAFDAC din ta ce bayan yada magungunan jabu wasu marasa kishin kasa har gurbata manja suke yi da wani sinadari wanda ke da illa ga hantar dan adam.

Jabun maganin maleriya na Coartem da kuma gangariya

Wannan bayani daga NAFDAC  ya zo a daidai lokacin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce a shekarun 2013 zuwa 2017 akwai bayanai da ke nuna cewa akasarin magungunan jabu na duniya anfi hada-hadarsu a yankin Afrika kudu da hamada. Rahoton ya kuma ce a duk shekara akalla mutane 64,000 zuwa 158,000 ke mutuwa a saboda shan maganin maleriya na jabu a kasashen namu na Afrika Kudu da Hamada.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply