Ministan tsaron Nijeriya Manjo Janar Bashir Magashi ya nemi dakarun sojin kasar su ƙara ƙaimi da nuna kishin kasa wajen yaƙar ayyukan ta’addanci.
Ministan ya yi wannan kira ne a wani taron bikin karrama jami’an soji da aka gudanar a makarantar horas da jami’an soji dake Zaria a jihar Kaduna.
Ministan ya nemi sojin ƙasar su kawar ɗabi’ar nan ta nuna son zuciya a yayin da suke gudanar da ayyukansu.
