Home Labarai Magidanci ya binne jikansa da rai a Bauchi

Magidanci ya binne jikansa da rai a Bauchi

218
0

Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta ce ta cafke wani magidanci mai suna Bawada Audu, a Rimin Zayam, karamar hukumar Toro da ke jihar bisa zarginsa da binne jikansa da ransa.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda na jihar Ahmed Wakil, Bawada ya amshe jaririn da ‘yarsa, Hafsat Bawada ta haifa ya kuma binne shi da rai a kusa da gidansa, kuma kungiyar kare hakkin dan Adam ce ta sanarwa da rundunar ‘yansandan jihar.

Ahmed Wakil ya bayyana cewa ‘yansanda sun garzaya wajen da lamarin ya faru, inda suka gaggauta tono yaron su ka kuma garzaya da shi babban asibiti, inda aka tabbatar da cewa ya mutu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply