Home Labarai Magidanci ya fada rijiya ya mutu a Kano

Magidanci ya fada rijiya ya mutu a Kano

94
0

Wani magidanci dan kimanin shekaru 65 da aka bayyana sunansa da Isah Amadu Kamilu mazauni sabuwar Unguwa da ke Rano ya gamu da ajalinsa biyo bayan fadawa rijiya da ya yi.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Mallam Saidu Muhammad ya tabbatar da cewa jami’ansu sun tarar da gawar Isa ne bayan da suka garzaya zuwa wurin don ceto rayuwarsa sakamakon kiran gaggawa da suka samu.

“Mun fahimci cewa Malamin mai shekaru 65 yana fama da larurori na rashin lafiya da dama ciki har da rashin gani wanda hakan ne ma ya yi sanadiyyar ya fada cikin rijiyar, ”inji shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply