Home Labarai Magidanci ya soka wa matarsa da wanta wuƙa bayan kotu ta raba...

Magidanci ya soka wa matarsa da wanta wuƙa bayan kotu ta raba aurensu

66
0

Rundunar ƴansanda ta jihar Kano ta kama Biliyaminu Abdullahi dan shekara 28 bisa zargin daɓa wa tsohuwar matarsa tare da wanta wuka jim kadan bayan wata kotu da ke Rano ta raba aurensu.

Yayin da ake tuhumarsa, Abdullahi ya bayyana cewa ya aikata hakan ne sakamakon rashin jindadin hukuncin da kotun ta yanke duk da rashin samunsa da laifi da kotun ta yi.

Abdullahi ya bayyana cewa suna zaman lafiya da matarsa kafin watan nata ya zo ya dauke ta ya maida ta gida, kuma bayan bin duk wasu hanyoyi da suka dace don ta koma taki komawa karshe suka maka shi kotu kan dole sai ya sake ta duk da sun kasa bayyana hujjar neman sakin.

Ya kara da cewa “mun je kotu 2 dukansu suna watsar da shari’ar har zuwanmu wannan kotun inda ta yanke hukuncin in karbi sadaki na ₦20,000 wanda naki yarda da hakan, shi ne kotun ta umurci matar ta kwashe kayanta daga gidana, wanda ni kuma na sareta da yayan nata don huce takaicina” injishi.

Matar mai suna Shafa’atu Sule mai dauke da tsohon ciki, ta bayyana cewa ba ta samun kulawa a gidan tsohon mijin nata, tare da shan zagi kullum ko ta yi laifi ko bata yi ba.

Kakakin rundunar ƴansanda na jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da afkuwar lamarin, wanda tuni kwamishinan ƴansanda na jihar Habu A. Sani ya bada umurnin ci gaba da bincike kan lamarin kafin tura wanda ake tuhuma zuwa kotu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply