Dakataccen mukaddashin hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa tu’annati EFCC Ibrahim Magu, ya nemi da babban sufeton ‘yansanda na Nijeriya Muhammad Adamu da ya ba da shi beli.
Tun ranar Litinin da ta gabata ne ake tsare da Ibrahim Magu da kwamiti na musamman da shugaban kasa ya kafa ke bincika kan zargin cin hanci.
Lauyansa Mr Oluwatosin Ojaomo ne ya nemi a ba da Magu beli a ranar Juma’ar nan.
