Home Labarai Da Dumi-Dumi: Mai Garin Radda ya kubuta daga hannun ‘yan bindiga

Da Dumi-Dumi: Mai Garin Radda ya kubuta daga hannun ‘yan bindiga

97
0

Bayanai da DCL Hausa ta tattara sun tabbatar mata da cewa Mai Garin Radda cikin karamar hukumar Charanci jihar Katsina da ‘yan bindiga suka sace a makon jiya ya kubuta.

Ahmad Mande wani dan aslain garin na Radda ya shaida cewa Mai Garin Alhaji Kabir Umar ya samu kubuta da daren Talata wayewar Laraba da yanzu haka ya ke a wani asibitin Kano domin duba lafiyarsa.

Sai dai har yanzu babu takamaiman bayanin ko kudin fansa aka biya sannan aka sako shi ko kuma tserewa ya yi daga hannunsu.

Kwanaki 4 dai Mai Garin ya kwashe a hannun wadanda suka sace shi, bayan da ‘yan bindiga suka kai hari a garin na Radda a ranar 22 ga wannan wata na Janairu.

Ko bayan sace shi da kwana daya, sai da iyalansa suka yi waya dashi yace yana cikin koshin lafiya a dajin Zamfara.

Labari Mai Alaka: An sace Mai Garin Radda a jihar Katsina

Kanin Mai Garin Radda da ‘yan bindiga suka harba a Katsina ya rasu

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply