Home Labarai Majalisa na ƙoƙarin hana ɗaukar ma’aikatan wucin gadi a Nijeriya

Majalisa na ƙoƙarin hana ɗaukar ma’aikatan wucin gadi a Nijeriya

44
0

Majalisar Dattawan Nijeriya ta fara duba kudirin dokar da ke neman hana ma’aikatu da kamfanoni daukar ‘yan Nijeriya da suka kammala karatu aikin wucin gadi.

Sanata Ayo Akinyelure daga jihar Ondo ne dai ya dauki nauyin kudirin, kamar yadda mai taikakawa shugaban majalisar Dattawan Ezrel Tabiowo ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ta Ambato Akinyelure na cewa ma’aikatu da kamfanoni da dama na ci gaba da fakewa da ayyukan wucin gadin don rage kudaden da suke kashewa, wajen daukar cikakkun ma’aikatan.

A cewarsa, kididdigar da suka samu daga kungiyar kwadagon Nijeriya NLC, ta nuna cewa da yawa daga cikin ma’aikatan da ke aiki a kamfanonin sadarwa da na mai da iskar gas, ma’aikatan wucin gadi ne.

Akinyelure ya yi gargadin yadda daukar ma’aikatan wucin gadin ke ci gaba da samun gindin zama a Nijeriya, ba tare da wani mataki na kawo karshen matsalar ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply