Home Labarai Majalisa ta amince da dokar tilasta gwaji kafin aure a Kano

Majalisa ta amince da dokar tilasta gwaji kafin aure a Kano

37
0

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da ƙudirin dokar tilasta gwaji kafin aure, don takaita yaɗuwar cututtuka.

FREEDOM RADIO tace majalisar, ta yi la’akari da yadda cututtukan da ke yaɗuwa tsakanin ma’aurata, a wasu lokutan ma har zuwa ƴaƴan su ke ƙara yaɗuwa, abinda ya tilasta mata amincewa da ƙudirin dokar.

Ɗan majalisa Musa Ali Kachako da ke wakiltar ƙaramar hukumar Takai a jihar Kanon wanda shi ne ya gabatar da ƙudirin dokar ya ce, wajibi ne majalisar ta samar da wannan doka, don inganta lafiyar jama’a.

DCL Hausa ta gano cewa wasu daga cikin al’ummar Kano sun yi maraba da wannan mataki na majalisar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply