Home Labarai Majalisa ta amince da gyaran kasafin kudin 2020 bayan ta kara N300bn

Majalisa ta amince da gyaran kasafin kudin 2020 bayan ta kara N300bn

84
0

A ranar Alhamis din nan ne, Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da kasafin kudin shekarar 2020 na N10.8 Tiriliyan da aka yiwa bita, kamar yadda majalisar wakilai ta amince da shi a ranar Laraba.

An amince da kasafin ne a zaman majalisar na yau bayan yin la’akari da rahoton kwamitin kasafi na majalisar wanda Sanata Barau Jibril ke jagoranta.

Majalisar dai ta kara yawan kasafin kudin daga N10.5trn da shugaban kasa ya gabatar mata, inda ta kara Naira Biliyan 300.

A cikin kasafin dai, za kashe Naira Tiriliyan 2.4 wajen gudanar da manyan ayyuka sai kuma Naira Tiriliyan 2.9 da za a kashe su wajen biyan bashi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply