Home Labarai Majalisa ta ba Akpabio wa’adi ya fallasa ‘yan majalisar da aka ba...

Majalisa ta ba Akpabio wa’adi ya fallasa ‘yan majalisar da aka ba kwangila

79
0

Majalisar wakilan Nijeriya ta ba ministan harkokin Niger Delta Godswill Akpabio wa’adin sa’o’i 48 ya buga sunayen ‘yan majalisar da suka amshi kwangila daga hukumar NDDC.

Idan dai za a iya tunawa a lokacin zaman kwamitin bincike kan barnatar da Naira Biliyan 40 daga hukumar ta NDDC, Akpabio ya ce kashi 60 na kwangilolin hukumar ana ba ‘yan majalisar ne.

Da yake bayani kan zargin a lokacin zaman majalisar, kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya kalubalanci ministan da ya buga sunayen kamfanoni, kudin kwangilar da wuraren da za a yi aikin da duk wasu bayanai da suka shafi biyan kudin kwangilolin.

Gbajabimila ya yi gargadin cewa rashin yin hakan zai janyo doka ta yi aikinta kan ministan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply