Home Siyasa Majalisa ta ba Buhari kwanaki biyar ya fitar da sunayen ministoci

Majalisa ta ba Buhari kwanaki biyar ya fitar da sunayen ministoci

103
0

Wallafarwar: RiT

 

 

Majalisar dattawa ta ba shugaba Buhari daga nan zuwa juma’a da ya mika sunayen mutanen da ya ke son nadawa ministoci a sabuwar gwamnatinsa domin tantance su.

Shugaban kwamitin yada labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Adedayo Adeyeye ya ce majalisar zata tafi hutu a ranar 26 ga watan yuli ta dawo ranar 26 ga watan satumba.Ya ce idan har sunayen basu iso a garesu ba daga nan zuwa juma’a, to yin hakan ba zai hana su bin tsarin majalisar na tafiya hutu. Jaridar The Punch ce ta fitar da wannan labari a rannan lahadin nan.

Adeyeye ya kara da cewa shugaban kasa yana da damar aiko da sunayen duk sadda yaso , aikin majalisa ne ta duba su kuma tayi aiki akansu ,domin ci gaban kasa. Sai dai Adedayo ya ce majalisa bata da damar matsawa shugaban kasa, don haka za’a iya kiransu duk sadda aka bada sunayen koda kuwa suna cikin hutu ne.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply