Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Majalisa ta ba TCN wa’adin kammala aikin lantarkin Kano

Majalisa ta ba TCN wa’adin kammala aikin lantarkin Kano

131
0

Kwamitin Majalisar Wakilan Nijeriya kan hasken lantarki ya ba kamfanin rarraba hasken lantarki TCN wa’adin watanni huɗu ya kammala aikin tashoshin lantarkin Kano guda biyu.

Tashoshin dai sun haɗa da ta Walalambe da ke ƙaramar hukumar Nasarawa da kuma Rimin-Zakara a ƙaramar hukumar Ungogo.

Shugaban kwamitin Magaji Da’u ya bada wa’adin lokacin ziyarar gani da ido da ya kai kan aikin a ranar Juma’a.

Da’u ya ce tashar Walalambe da aka ƙirƙiro shekaru 15 da suka wuce za ta samar da lantarki ne ga kamfanoni da al’ummar yankin Dakata yayin da ta Rimin-Zakara za ta ƙarfafa samar da lantarki a cikin Birni.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply