Home Labarai Majalisa ta bukaci Buhari ya sauke Hafsoshin Tsaro

Majalisa ta bukaci Buhari ya sauke Hafsoshin Tsaro

141
0

Ƴan majalisar Dattawa sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sauya Hafsoshin Tsaron ƙasar domin shawo kan matsalar tsaro da ake fama da ita.

Wannan shi ne karo na biyu da majalisar ta bukaci yin hakan tun watan Yulin da ya gabata, har zuwa jiya da Sanata Kashim Shettima na Borno ya sake kawo kudurin a majalisar bayan kisan manoma 67 da ya faru a jiharsa ta Borno.

Majalisar ta kuma bukaci Shugaba Buhari ya gaggauta kawo wani sabon salo na ganin an magance matsalar tsaron, ta hanyar daukar ƴansakai JTF 10,000 tare da daukar sabbin ma’aikata masu yawa a bangaren ƴansanda da kuma sojojin kasar nan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply