Majalisar dattawa ta bukaci shugaban Nijeriya Muhammad Buhari da ya yi wa ‘yan kasa jawabi kan zanga-zangar da ke wakana yanzu haka a sassan kasar.
Kazalika, majalisar ta kuma bukaci ‘yansanda da su ba da kariya ga masu zanga-zanga domin hana bare-gurbi yin amfani da damar su aikata assha.
Majalisar ta dauki wannan matakin ne biyo bayan kudiri da Sanata Biodun Olujimi ya gabatar na a sake fasalta tsarin zanga-zangar EndSARS.
