Home Labarai Majalisa ta tabbatar da Sarki Aminu, shugaban sarakunan Kano na din-din-din

Majalisa ta tabbatar da Sarki Aminu, shugaban sarakunan Kano na din-din-din

265
0

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da yin gyara ga kundin dokar masarautun.

Gyaran dokar dai, zai ba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero damar zama shugaban sarakunan Kano na din din din.

A baya dai, dokar ta samar da tsarin karɓa-karɓa ne na tsawon shekaru biyu tsakanin sarakunan jihar.

Shugaban masu rinjaye na majalisar Kabiru Hassan Dashi ne ya jagoranci gabatar da ƙudirin a gaban majalisar a ranar Litinin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply