Home Labarai Majalisa ta tabbatar da sabbin alkalan kotun koli 8

Majalisa ta tabbatar da sabbin alkalan kotun koli 8

119
0

Majalisar dattawa ta tabbatar da sabbin alkalan kotun koli 8 da shugaba Buhari ya aike mata na neman ta amince da su.

Shugaba Buhari a cikin wasikar da ya aike wa majalisar da shugabanta Ahmad Lawan ya karanta, ya ce an zakulo sunayen mutanen ne bisa cancanta da kuma shawarwarin da majalisar alkalai ta kasa ta bada.

Ya kuma hakan na da hurumi a sashe na 231 karamin sashe na 2 cikin baka na kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Wadanda aka tabbatar din su ne, Lawal Garba, Helen Ogunwumiji da MM Saulawa.

Sauran su ne Adamu Jauro, Samuel Oseji, Tijjani Abubakar da Emmanuel Agim.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply