Home Labarai Majalisa ta yi tir da rashin zuwan Buhari

Majalisa ta yi tir da rashin zuwan Buhari

142
0

Shugabannin marasa rinjaye a majalisar wakilai ta tarayya sun bayyana rashin halartar shugaban kasar a gaban majalisar a matsayin abun da zai kara masa bakin jini ga ‘yan Nijeriya da ma sauran duniya.

A cikin wata sanarwa da suka fitar ta hannun shugaban marasa rinjaye na majalisar Ndudi Elumelu, ‘yan majalisar sun yi tir da ikirarin da babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami ya yi na cewa majalisar ba ta da ‘yancin gayyatar shugaban kasar.

Majalisar dai ta gayyaci Buharin ne domin ya yi mata bayani kan matsalolin tsaro da kasha-kashi da kuma ayyukan ta’addanci da kasar ke fama da shi.

Elumelu, ya ce zance da ministan shari’ar ya yi, ya nuna cewa kamar bai da masaniya ga dokokin da kuma halin da ake ciki a cikin kasar.

A cewarsa, sashe na 218 da Ministan ya fake da shi, da kuma sashe na 88 da na 89, sun bayyana karara, yadda majalisar kasar ke da ikon neman shugaban kasar ya yi mata bayanin yadda yake tafiyar da harkokin tsaron kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply