Home Labarai Majalisa za ta sanya hukuncin daurin rai da rai ga masu fyade

Majalisa za ta sanya hukuncin daurin rai da rai ga masu fyade

69
0

Majalisa za ta sanya hukuncin daurin rai da rai ga masu fyad

Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta bada shawarar zartas da hukuncin daurin rai da rai ga masu fyade a jihar.

Kakakin Majalisar Ibrahim Abdullahi ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da majalisar ke tattaunawa kan rahoton da kwamitin haɗin guiwa na ɓangaren shari’a da kula da harkokin mata ya gabatar kan buƙatar samar da dokar.

Kudirin wanda kakakin majalisar ya dauki nauyin gabatarwa zai zama hanyar dakile cin zarafin mata musamman fyade a fadin jihar.

Tun da fari, kudirin ya samu sahalewar shugaban masu rinjaye Tanko Tunga tare da mataimakin shugaban marasa rinjaye Luka Zhekaba.

Za a yi wa wannan doka karatu na ukku a 21 ga watan Disambar wannan shekarar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply