Home Labarai Majalisar Dattawa na yinkurin kafa hukumar gyaran tarbiyyar tubabbun Boko Haram

Majalisar Dattawa na yinkurin kafa hukumar gyaran tarbiyyar tubabbun Boko Haram

64
0

Majalisar dattawa ta gabatar da wani yinkuri na kafa hukumar da za ta gyara rayuwar tubabbun ‘yan ta’adda a zaman ta na yau Alhamis.

Wannan ya biyo bayan kudirin da Sanata Ibrahim Gaidam, mai wakiltar Yobe ta Gabas ya gabatar a yau.

A watan da ya gabata ne dai, rundunar sojin kasar ta ce kimanin mayakan Boko Haram 608 ne ake aikin gyaran tarbiyyar su a karkashin shirin tan a Safe Corridor da ke Malam-Sidi na jihar Gombe, bayan sun mika wuya tare da aje makaman su.

Daga cikin ayyukan da ake na gyaran tarbiyyar ta su, sun hada da koyar da su karatun book da na addini, da koyar da sana’o’i da kuma kula da lafiyar su da kyautata tunanin su.

Saidai kuma wasu tawagar dattawan Borno da suka ziyarci wurin a bara, karkashin jaogarancin tsohon gwamnan jihar Kashim Shettima, sun nuna damuwa da yanayin aikin sojojin, wajen gyaran tarbiyyar ta su, tare da nuna fargabar idan har tubabbun ‘yan ta’addan suka sake shiga mutane za su iya komawa ruwa.

Sun kuma bukaci shugaba Buhari ya dakatar da shirin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply