Home Labarai Majalisar Dattawa ta bukaci hafsohin tsaro su yi murabus

Majalisar Dattawa ta bukaci hafsohin tsaro su yi murabus

119
0

Majalisar dattawan Nijeriya ta yi kira ga manyan hafsoshin tsaron kasar da su sauka domin samun sabbin hanyoyin yaki da matsalar tsaron kasar.

Wannan kira ya biyo bayan wani batu da Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya gabatar a zaman majalisar kan karuwar mutuwar sojoji da sauran jami’an tsaron da ake samu.

Majalisar ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da kayan yaki na zamani domin karfafa ayyukan sojojin.

Da yake magana da ‘yan jarida kafin karshen zaman majalisar, Sanata Ndume ya kafe da cewa kira ga hafsoshin tsaron su yi murabus ba shi ne kudirin da ya gabatar ba, saidai an kara shi ne, kuma ya samu amincewar majalisar ba tare da son ran shi ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply