Home Labarai Majalisar Dattawan Nijeriya ta nuna damuwa kan tafiyar hawainiya kan hanyar Abuja-Kaduna-Kano

Majalisar Dattawan Nijeriya ta nuna damuwa kan tafiyar hawainiya kan hanyar Abuja-Kaduna-Kano

73
0

Kwamitin Ayukka na majalisar Dattijan Nijeriya ya koka kan tafiyar hawainiyar da aikin sabunta babbar hanyar Abuja-Kaduna-Zari’a-Kano.

Shugaban kwamitin Sanata Muhammad Adamu Aliero ya bayyana hakan a yau Litinin, lokacin da ya jagoranci tawagar kwamitin zuwa wata ziyarar gani da ido da suka kai a inda ake aikin.

Tun a ranar 20 ga watan Disamban shekarar 2017 ne aka ba kamfanin Julius Berger kwangilar aikin kan N155.48bn.

Aliero ya bayyana damuwar sa kan yadda aikin ke tafiyar hawainiya, yana mai cewa ya takaita harkoki a yanken arewacin kasar, musamma ganin yadda ya karade shiyyoyi uku na yankin.

Sanatan ya nuna shakkun yiwuwar kammala aikin a cikin watanni 14 da suka rage.

 

Da yake nuna rashin gamsuwa ga yadda aikin ke tafiya Sanata Kabir Barkiya daga jihar Katsina ya nuna damuwa kan yadda rashin kammala aikin ke janyo salwantar rayukan jama’a.

A nasa jawabin manajan kamfanin Mr Benjamin Bott ya ce kamfanin na da kyakkywar shaida kan gudanar da ingantaccen aiki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply