Home Sabon Labari Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kafa karin masarautu a...

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kafa karin masarautu a jihar

82
0

Abdullahi Garba Jani

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kudirin dokar nan da ke neman a kafa karin masarautu a jihar.

A ranar Litinin ta wannan makon ne dai sashen zartaswar jihar ya aike da kudirin dokar, wanda ya samu karatu na 3 a ranar Alhamis din nan, kuma aka amince da shi.

Jaridar *Daily Nigerian* ta ba da rahoton cewa a sashe na 12 ne kadai aka yi wa kwaskwarima, wanda ‘yan majalisar suka saka wata dokar da ke cewa dole ne sai gwamnan ya nemi amincewarsu kafin ya zartar da hukuncin kafa sarakunan masu daraja ta daya, ta biyu da ta uku.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply