Home Sabon Labari Majalisar Kogi ta fara yunkurin tsige mataimakin gwamna

Majalisar Kogi ta fara yunkurin tsige mataimakin gwamna

70
0

Nuruddeen Ishaq Banye/AGJ

A ranar Talata da ta gabata ne majalisar dokokin jihar Kogi da ke Arewa ta tsakiyar tarayyar Nijeriya, ta fara yunƙurin tsige mataimakin gwamnan jihar Simon Achuba, bisa zargin yin zagon ƙasa.

Jaridar _Daily Trust_ ta ruwaito cewa wannan yunƙuri na zuwa ne, a daidai lokacin da alaƙa tsakanin gwamnan jihar da mataimakin sa ke ƙara tsami.

A zaman da ‘ƴan majalisar suka gudanar a a ranar Laraba , sun bayyana kalaman da mataimakin gwamnan ya yi a wata hira da aka yi da shi a gidajen talabijin na _Channels_ da _AIT_ a matsayin abun takaici, kuma zagon ƙasa ga gwamna Yahaya Bello da jama’ar jihar Kogi.

Majalisar Jihar Kogi

Shugaban masu rinjaye na Majalisar Abdullahi Bello wanda ke wakiltar mazaɓar Ajaokuta ne dai ya gabatar da takardar buƙatar tsige mataimakin gwamnan, wadda ta samu sa hannun ‘ƴan majalisa 21 daga cikin 25 na jihar.

Da yake zartar da matsaya kan buƙatar, kakakin majalisar dokokin jihar Mathew Kolawole ya amince da buƙatar inda ya bada umurnin da a aike wa mataimakin gwamnan da takardar domin ya kare kan sa a cikin kwanaki 14.

Saidai a nata bangaren jam’iyyar adawa ta PDP a jihar, a ta bakin mai magana da yawunta Prince Bode Ogunmola ta yi watsi da wannan yunƙuri da ta bayyana ƙoƙarin ɓata wa mataimakin gwamnan suna.

A ranar 21 ga watan Nuwamba mai zuwa ne dai za a gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokikin jihar Kogi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply