Majalissar dokokin kasar Tchadi ta karrama Shugaban kasar Gen Idriss Deby Itno da matsayin Marshal.
Shugaban majalisar Haroun Kabadi ya ce Shugaban ya cancanci a karrama shi bisa la’akari da kokarin da ya ke yi na ganin an tabbatar da dakile ayyukan ta’addanci a ciki da wajen kasar.
Ko a watan Maris din shekarar nan an ga Shugaba Idriss Deby sanye da kayan Sarki yana jagorantar dakarun sojin kasar inda suka fatattaki yan kungiyar Boko Haram a yankin tafkin Tchadi.
Shugaban mai kimanin shekaru 68 ya shafe kusan shekaru 30 yana Shugabancin kasar ta Tchadi.
