Home Labarai Majalisar wakilai za ta ɗau mataki kan hana ƴan Nijeriya shiga Amirka

Majalisar wakilai za ta ɗau mataki kan hana ƴan Nijeriya shiga Amirka

130
0

Majalisar wakilai ta tarayya na kokarin samo hanyoyin diplomasiyya da zai daidaita matakin Amurka na hana ‘yan Nijeriya shiga kasar.

‘Yan majalisar za su gana da hukumomin gwamnati da na diflomasiyya don gano dalilan saka wannan doka da domin daukar matakan hana faruwar hakan.

Sun kuma yi kiraga majalisar shugaba Muhammadu Buhari su dauki matakan da suka dace don ganin an soke wannan mataki.

Wannan ya biyo bayan amincewa da wani kudiri da Yusuf Tajudeen ya gabatar a zaman majalisar na jiya da Femi Gbajabiamila ya jagoranta.

Yusuf ya ce Amurka ta sanya Nijeriya a jerin kasashen da aka takaita shigar su kasar tare da Tanzaniya, Sudan, Eritrea, Myanmar da Kyrgrzstan a ranar 31 ga watan Janairu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply