Ƴan majalisar wakilai za su dawo zaman majalisar a ranar Talata.
Maga-takardan majalisar Patrick Giwa ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Haka kuma, Giwa ya ce ma’aikata da sauran mataimakan ƴan majalisar za su yi aiki ne daga gida, yayin da za a sanar da su lokacin da ake buƙatar su zo aiki.
A cikin watan Maris ne dai majalisar ta dakatar da zaman ta na tsawon makonni biyu domin taƙaita cutar coronavirus, kafin daga bisani a tsawaita hutun saboda dokar hana fita da aka sanya a wasu jihohin.
