Home Labarai Mako na musamman ga zaman lafiyar kudancin Kaduna

Mako na musamman ga zaman lafiyar kudancin Kaduna

114
0

Gwamnatin jihar Kaduna ta sassauta dokar hana zirga-zirga ta ba dare ba rana a ƙananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf.

Kwamishinan tsaron jihar Mr Samuel Aruwan ne ya bayyana haka yayin da yake karanta sanarwar a gaban manema labarai a cikin mako mai ƙarewa, inda ya ce dokar za ta fara aiki daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safiyar ko wace rana.

Kazalika a cikin makon nan ƙabilun kudancin Kaduna da ke rigima da junansu, sun haɗu a wani sansanin ‘yan gudun hijira inda har wasunsu suka zubar da hawaye kan yadda rikicin ƙabilanci da addini ya raba kawunansu cikin shekaru 40 da fara rikicin a yankin.

Ko a makon jiya gwamnatin jihar ta Kaduna ta sassauta dokar hana fita da ta sanya a wasu ƙananan hukumomi biyu da ke kudancin jihar da suka haɗa da Ƙaura da Jama’a, inda a baya-bayan nan ake yawan samun hare-haren ramuwar gayya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply