Home Labarai Makomar Matawalle: Kotun Koli ta dage shari’ar APC zuwa ranar 2 ga...

Makomar Matawalle: Kotun Koli ta dage shari’ar APC zuwa ranar 2 ga Maris

61
0

Kotun kolin Nijeriya ta dage sauraron karar da jam’iyyar APC ta shigar, wadda ke neman kotun ta yi bitar hukuncin da ta yanke a ranar 24 ga watan Mayun bara, na soke zabukan ‘yan takarar jam’iyyar suka lashe na 2019 a jihar Zamfara.

Jam’iyyar ta APC da sauran masu shigar da kara, wadanda Chief Robert Clarke SAN ke wakilta, na kalubalantar Sanata Kabiru Marafa da sauran mutane 179.

Clarke ya bukaci a dage sauraron karar ne domin samun damar sanar da wadanda ake kara daga 141 zuwa 148.

Kwamitin alkalai biyar, karkashin jagorancin alkalin alkalai Tanko Muhammad, sun dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Maris, domin ba wanda ke kararar damar isar da sammace ga wadanda ake karar da ba su halarci kotun ba, kuma ba su turo wakilan su ba.

Lauyan dai ya sake shigar da karar ne, bayan tun da farko kotun kolin ta yi watsi da ita a ranar 22 ga watan Agustan bara.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply