Kungiyar malaman kwalejojin ilimi ta kasa (COEASU) ta yi gargadin fara gudanar da yajin aikin sai baba ta gani dangane da zargin da ta ke na yin watsi da harkokin da suka shafi walwalar membobin ta da gwamnatin Nijeriya ta ke yi.
Shugaban Kungiyar ta COEASU Kwamared Nuhu Ogirima ne ya bayyana haka ya yin da ya jagorantanci wani taro da kungiyar ta gabatar a safiyar Alhamis din makon nan.
Kwamared Ogirima ya ce kungiyar ta ba gwamnatin tarayya wa’adin makonni 3 da ta warware matsalolinta da suka hada da yankewa membobin kungiyar albashi dama tilasta su shiga sabon tsarin nan na biyan albashi na bai daya wato (IPPIS).
