Home Labarai Malamin makaranta ya kashe ƴansanda 3

Malamin makaranta ya kashe ƴansanda 3

32
0

Kotun majistire dake garin Makurdi a ranar Talatar nan ta tsare wani malamin makaranta Mernyi Christopher a gidan gyaran hali bisa zarginsa da kashe ƴansanda 3.

Rundunar ƴansandan na tuhumar Christopher mazaunin karamar hukumar Katsina-Ala a jihar Benue da hada kai da ƴanta’adda da fashi.

Mai gabatar da kara na ƴansanda Sajen Ato Godwin ya shaidawa kotun cewa tawagar Operation Zenda ne suka samu damar cafke Christopher bayan ya dade yana aikata ta’asa a yankin na Katsina-Ala.

Ya kuma shaida wa kotun cewa a ranar 24 ga watan Disambar 2020 Chirstopher da jama’arsa sun kai hari gidan shugaban karamar hukumar Katsina-Ala inda suka kashe ƴansanda 3 tare da sace bindigunsu kirar AK47.

Yayin tuhumarsa, Christopher ya amsa laifinsa wanda ya ce ya aikata tare da taimakon abokin aikinsa Aondofa Chekele da sauran yaransa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply