Home Lafiya Maleriya: AN SOMA FESHIN MAGANIN SAURO A ARGUNGU

Maleriya: AN SOMA FESHIN MAGANIN SAURO A ARGUNGU

81
0

Wata kungiya mai hankoron ganin ta kyauta tawa al’umma wato (Good Samaritan society of Nigeria) ta soma wani aikin feshin magani a unguwannin garin Argungu na jihar Kebbi.

Hotan daya daga cikin mambobin kungiyar Good Samaritan society of Nigeria ta Argungu jihar Kebbi ke nan ke feshin sauro a wata kwata

 

 

Kungiyar tana aikin feshin a unguwanni da wuraren da kwatoci suke da kuma magudanun ruwa, inda suke ganin nan ne matattarar sauro wanda ka iya haifar da cutar maleriya.

 

Masu sharhi dai na ganoin irin wannan mataki da kungiyar Good Samaritan society of Nigeria ta dauka zai iya rage yawaitar cutar zazzabin cizon sauro wace a ‘yan shekarun ke taba lafiyar jama’a a birane da yankunan karkara.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply