Shugabannin sojin da ke jagorantar kasar Mali sun aminta da cewa za su gudanar da mulkin rikon-kwarya na tsawon watanni 18 har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe.
Mai magana da yawun tawagar sojin Moussa Camara ya ce soji ko farar hula ne zai jagoranci gwamnatin rikon-kwaryar.
Sojojin sun yanke wannan shawarar ne bayan wani zama na kwanaki uku da suka gudanar domin cimma matsayar yadda za a dawo da mulkin farar hula a kasar.
