Home Labarai Mallakar bindiga abu ne mai sauki – Awwalun Daudawa

Mallakar bindiga abu ne mai sauki – Awwalun Daudawa

47
0

Dan bindigar nan da yace ya tuba ya ajiye makamai, Awwalun Daudawa, yace cikin ruwan sanyi suke samun bindiga, kamar yadda wani ka iya zuwa sayen biredi.

A cikin wata ganawa da ya yi da Daily Trust, Awwalun Daudawa, yace yana samun bindiga ne ba tare da ya sha wahala ba.

Awwalun Daudawa yace rashin adalci da aka taba shifka masa ne ya sa shi tsunduma harkar ta’addanci.

Ya labarta cewa a zamanin gwamnatin jihar Zamfara da ta gabata ne aka zo aka kwashe masa shanu bisa zargin na sata ne. Ya fada wa jami’an tsaro a lokacin cewa ko daya babu na sata, ya gaje su ne wajen iyayensa.

DCL Hausa ta gano cewa bayan kwace masa shanun nan da yace an yi masa ne ya sayar da sauran kadarorinsa ya sayo bindiga domin kamar yadda yace ya rika ciyar da iyalinsa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply