Home Sabon Labari Maman Taraba Ta Koma Jam’iyyar PDP

Maman Taraba Ta Koma Jam’iyyar PDP

65
0

Siyasa: Mama Taraba ta koma PDP.

Tsohuwar ministar harkokin mata ta Nijeriya Hajiya Aisha Jummai Alhassan ta ce ta kammala shiri tsaf domin komawa jam’iyyar PDP.

Jummai Alhassan dai ita ce ‘yar takarar gwamnan jihar Taraba a karkashin jam’iyyar UDP a zaben 2019 inda ta samu kuri’u dubu 14,651.

Tsohuwar ministar dai ta koma jam’iyyar UDP ne bayan da gaza samun tikitin tsayawa takara a jam’iyyar APC, jam’iyyar da ta tsaya takara a 2015 har ta samu kuri’u dubu 275,966 ta zo ta biyu a zaben gwamna na shekarar.

Bayan ta fadi zaben 2015 din ne shugaban kasa Buhari ya nada ministar harkokin mata, amma daga bisani ta yi murabus bisa yamadidin biyayyarta ga jam’iyyar adawa.

Mama Taraba ta fada wa manema labarai a birnin Jalingo bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar UDP cewa mafi yawan magoya bayanta a mazabu 168 ne suka karfafa ma ta guiwar ta koma PDP.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya ba da rahoton cewa Hajiya Jummai Alhassan ta nemi takarar kujerar sanata mai wakiltar Taraba ta Arewa a shekarar 2011 kuma ta yi nasara a karkashin jam’iyyar PDD kafin daga bisani ta sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a shekarar 2015.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply