Home Sabon Labari Man City ta lallasa Aston Villa

Man City ta lallasa Aston Villa

80
0

Kulob ɗin Manchester City na ƙasar Ingila yayi nasara a kan Aston Villa da ci 6-1 a filin wasa na Villa Park da yammacin ranar Lahadi.

Dan wasan City Riyad Mahrez shi ne ya fara jefa kwallon a raga ana mintuna goma sha takwas da take wasa.

Sergio Aguero ya kafa tarihi inda ya ci kwallaye uku rigis ya kuma shiga sahun ‘ya gaba gaban masu cin kwallaye uku jimilla a wasa daya (Hatrick).

Kwallayen da Aguero ya ci sun haura na tsohon ɗan wasan Arsenal Thierry Henry.  Ya zuwa yanzu yayi kan-kan-kan da  Frank Lampard wanda yaci kwallaye 177 a tarihin gasar ta firimiya.

Ko a watan Fabrairun shekarar 2016 Aston Villa tayi rashin nasara da ci 6-0  a hannun Liverpool a filin wasa na Villa Park.

Da wannan sakamako Manchester City ta koma matsayi na biyu a kan teburin gasar, da tazarar maki 14 tsakaninta da Liverpool wadda ke ci gaba da zama a saman tebur.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply