Home Kasashen Ketare Man City ta lallasa Liverpool da ci 4-1

Man City ta lallasa Liverpool da ci 4-1

33
0

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta casa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a gidanta da ci 4-1 a gasar Firimiyar Ingila.

An dai shafe mintuna 45 din farko babu kungiyar da ta samu damar zura kwallo a ragar abokiyar hamayyarta.

Nasara da City ta samu kan Liverpool ta kara sanya wa kungiyar dada kare kambunta na buga wasanni 13 ba tare da an doke ta ba.

Yanzu dai Liverpool na a mataki na 4 da maki 40 a wasanni 23 da ta buga, ya yin da Man City ke jagorancin teburin gasar da maki 50 da kuma kwantan wasa daya da bata buga ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply