Home Labarai MAN ta roki gwamnatin Nijeriya ta bude iyakokin ta

MAN ta roki gwamnatin Nijeriya ta bude iyakokin ta

88
0

Kungiyar masu kere-kere ta Nijeriya MAN ta sake yin kira ga gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar sake buda iyakokin kasar ga sahihan ‘yan kasuwa masu shigo da kayayyaki.


Shugaban sashen bunkasa fitar da kayayyaki na kungiyar Ede Dafinone ya yi wannan kira a wajen wani taron karawa juna sani da hukumar bunkasa fitar da kayayyaki ta shirya a Lagos.

Ya ce ‘yan kungiyar sun zauna da gwamnati kuma sun fahimci kokarin ta na magance matsalar shigo da haramtattun kayayyaki a kasar, amma dai duk da haka akwai bukatar bada dama ga ‘sahihan ‘yan kasuwa da ke bukatar yin kasuwancin su da kasashe makwabta.

Dangane da taron karawa juna sanin, da kuma kaddamar da cibiyar kyautata kasuwanci, da cinikayyar intanet na majalisar dinkin duniya, Dafinone ya ce saukin isar da kaya ga abokan hudda a yankin yammacin Afrika harma turai da yankin Amirka ya ta’allaka ne ga irin saukin shige-da-fice da masu safarar kayan suka samu.

Da yake magana kan kare tattalin arzikin kasar, Dafinone ya ce gwamnati na yin dukkan mai yiwuwa wajen saukaka kasuwancin shige-da-ficen kayayyaki da musamman don taimakawa kasar fadada hanyoyin tattalin arziki daga man fetur.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply