Home Sabon Labari Manchester City ta sake jefa rashin tabbas ga makomar Lampard a Chelsea 

Manchester City ta sake jefa rashin tabbas ga makomar Lampard a Chelsea 

132
0

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta lallasa Chelsea da ci 3-1.

City ta yi nasarar jefa kwallaye 3 ringis a ragar Chelsea tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, dan wasan City Ilkay Gundögan ne dai ya fara zira kwallo a ragar Chelsea ana minti 18 da take wasa, sai kuma Phil Foden ya ci wa Cityn kwallonta ta biyu a minti na 31, kana daga bisani Kevin De Bruyne ya kara sharara kwallo ta 3.

Chelsea ta samu damar zira kwallo ta hannun dan wasanta Hudson.

Da wannan sakamako dai City ta dawo mataki na 5 a teburin gasar, inda Chelsea ke a mataki na 8 da maki 26 jimilla a wasanni 17 da ta doka a kakar firimiyar bana.

Wannan dai ya ƙara janyo cecekuce tare da matsin lamba ga makomar kocin Chelsea Frank Lampard saboda rashin kataɓus da ƙungiyar ke nunawa a baya bayan nan, duk kuwa da irin sayayyar ƴan wasan da suka yi a farkon kaka.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply