Home Sabon Labari Manchester ta yi biji-biji da Chelsea

Manchester ta yi biji-biji da Chelsea

68
0

Daga Ahmadu Rabe Yanduna

Manchester United ta lallasa Chelsea da
ci 4-0 a karawar ƙungiyoyin ta farko a kakar firimiya ta shekarar 2019-20.

Wannan lallasawa da akayi ma Chelsea ta bada mamaki ganin yadda ake yima kungiyar Chelsea din kallon zata ba maras da kunya.

Sabon kocin Chelsea Frank Lampard yayi rashin Nasara a karon farko yayin jagorantar kungiyar.

Manchester sun tabbatar da nasarar su kan Chelsea a wasan farko na firimiya da Frank Lampard ya jagoranci Chelsea a Old Trafford jiya Lahadi.

Man U ta samu ƙwallayen ta ne ta hannun Marcus Rashford da ya ci ƙwallaye biyu, da kuma Anthony Martial da Daniel James da suka ci ƙwallaye kowanen su.

Bayan kammala wasan mun ji ta bakin wasu magoya bayan ƙungiyar ta Chelsea a kan wannan rashin nasara inda Sageer Muhammad Sarkin Bai ya bayyana cewa, ” rashin samun nasara ga Chelsea bai zo masa da mamaki ba ganin yadda aka damka ragamar horas da kungiyar a hannun koci farin shiga da kuma girman ƙungiyar ta Chelsea a duniyar Ƙwallon ƙafa.

Haka shima wani mai goyon bayan Chelsea da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa ”kungiyar ta yi babban kuskure wajen sayar da manyan ƴan wasa irin su #Eden_Hazard bayan da kungiyar ta san an haramta mata sayen sabbin ƴan wasa a kakar bana.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply