Home Labarai Manoma a Nijeriya na roƙon gwamnati ta yafe masu bashin shekaru 16...

Manoma a Nijeriya na roƙon gwamnati ta yafe masu bashin shekaru 16  

238
0

Manoman yankin Arewa maso yammacin Nijeriya sun koka da cewa ba za su iya biyan bashin da suka karɓa hannun gwamnatin tarayya, tun daga shekarar 2005 zuwa 2016 ba.

Manoman sun nuna rashin kyawon anfani gona da kuma ƴan matsaloli da aka samu na ƙarancin ruwan sama da lalacewar anfani gona na daga cikin abunda ya haifar masu da asara har ya zamana ba za su iya biyan bashin ba.

Yanzu haka shugaban ƙungiyar manoman jihar Sakkwato Dr. Murtala Gagado ya roƙi gwamnatin tarayya ta yafe masu wannan bashi, inda ya bayyana cewa bashin na shekaru da dama galibin manoman su ba za su iya biyan sa ba, sai dai ko a sayar da gonakin manoman na su.

To amma ga kwararri ta bangaren noma irin su Farfesa Umar Aliyu shugaban tsangayar koyar da aikin gona a Jami’ar Usmanu Danfodiyo na ganin akwai bukatar a samar da kyakkyawan tsari kan yanayi kula da kuma karɓar bashi ga manoma a Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply