Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Manoma sun arce da bashin babban bankin Nijeriya CBN

Manoma sun arce da bashin babban bankin Nijeriya CBN

137
0

Akalla manoma 3,383 a jihar Taraba suka yi batan-dabo da kudin bashi N364m da suka karba daga babban bankin Nijeriya CBN a shekarar da ta gabata, 2019.

Mukaddashin shugaban kungiyar manoman shinkafa ta Nijeriya, reshen jihar Taraba, Tanko Andami ya bayyana hakan, inda ya ce manoman sun karbi bashin ne tsakanin 2018 da 2019 don noman rani, sannan aka neme su daga baya domin biyan bashin aka rasa.

Jaridar Muryar ‘Yanci ta rawaito cewa kudin da manoman kungiyar suka karba bashi sun ki biya, kuma da dama cikinsu sun gudu.

Andami ya bayyana mamakin dalilin da zai sa manoma su ki cika alkawuran da suka dauka na biyan bashin da suke da tabbacin sun amsa.

Babban Bankin Najeriya CBN ya ba su bashin ne domin inganta noman shinkafa cikin manufar gwamnatin tarayya na ciyar da kasa da shinkafa ba tare da an shigo da ita daga kasar waje ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply