Home Lafiya Manoma Sun Fi Kowa Samun Damar Saduwa Da Iyali-Bincike

Manoma Sun Fi Kowa Samun Damar Saduwa Da Iyali-Bincike

71
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”x8cnkiqb3″ data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”idtrcls0b” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”oae03b6pep” animation_delay=”0″]

Wani sabon bincike ya nuna cewa manoma sun fi kowane irin aiki samun sukunin yin jima’i yayin da wadanda ke layin karshe a binciken ke cewa su sau daya kawai suke samun yin jima’i a wata guda. Binciken ya ce ba wai shanu da kaji kawai ake kyankyasa a gona ba, tun da manoma na samun damar kusantar iyalansu akankari.

Jaridar New York Times ta ruwaito cewa kaso 67 na manoma da masu binciken suka tattauna da su, sun ce suna samun rayuwa mai inganci akan gado, acewar kamfanin samar da kayan ‘yar tsana na jima’i mai suna Lelo.

Wata kwararriya akan ilimin jima’i Kate Moyle ta ce hakan zai iya faruwa domin manoma suna motsa jikinsu fiye da sauran jama’an da ke zaune a birane wadanda ke aikin ofis, a saboda haka za su fi sauran jama’a kwazo.

Rahoton ya ce masu zanen gidaje su ne ke bin manoma a cikin jerin masu sana’o’in da suka fi samun damar saduwa da iyali. Daga nan sai kuma masu gyaran gashi.

Lelo mai wannan bincike ta tambayi mutane 2000 maza da mata a Birtaniya akan dangantakar ayyukansu da jima’i. Sai dai binciken nata ya nuna cewa ‘yan jarida su ne ke a layi na karshe domin ba sa samun damar kwanciya da iyali yadda ya kamata. Acewar binciken wasunsu sau daya kadai suke samun sukunin kwanciya da abokanan zamansu.

 

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply